Connect with us

News

Kazafin Satar Mace Ya Janyo Wa Dan Acaba Duka

Published

on

vllkyt6faoiefddud

Wani dan acaɓa ya sha da ƙyar bayan wata fasinja da ya ɗauka ta yi zargin cewa ya yi yunƙurin sace ta, lamarin da ya haddasa masa mummunan duka daga hannun fusatattun jama’a.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan matar ta wallafa zargin a shafukan sada zumunta, inda hakan ya tayar da hankalin mazauna yankin tare da jawo taruwar jama’a da suka afka wa dan acaɓan.

Advertisement

Ƙarancin Ruwa Ya Tilasta Wa Mazauna Wasu Ƙauyukan Kano Shan Ruwan Da Karnuka Ke Wanka A Ciki

Sai dai rundunar ’yan sandan jihar ta ce binciken farko da ta gudanar bai gano wata hujja da ke tabbatar da zargin da aka yi wa direban ba.

Advertisement

Kakakin rundunar, DSP Abayomi, ya bayyana cewa zargin da matar ta yi ba shi da tushe ko makama, yana mai cewa jami’an ’yan sanda na ci gaba da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru da kuma ɗaukar matakin doka da ya dace.

Ya ƙara da cewa an kai direban acaɓan asibiti domin samun kulawar likitoci bayan raunukan da ya samu sakamakon dukan da aka yi masa.

Advertisement

Rundunar ta yi kira ga jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu, tana mai jaddada cewa zarge-zarge na buƙatar cikakken bincike kafin a kai ga yanke hukunci.

 

Advertisement

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending