Connect with us

News

Kotun Daukaka Kara Ta Haramtawa INEC Karbar David Mark Matsayin Shugaban Jam’iyyar ADC 

Published

on

ADC

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin da ya hana hukumar zaɓe ta ƙasa INEC amincewa ko shiga cikin duk wani taron zaɓen shugabannin jihohi na jam’iyyar ADC da kwamitin riƙon ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark ya shirya.

A hukuncin da a ka yanke da rinjayen alƙalai biyu cikin uku, mai shari’a Okon Abang ya ce kotun ba ta ga wani dalili da zai sa ta soke umarnin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar tun ranar 29 ga Afrilu.

Wasu Ɓata Gari Sun Hallaka Mai Sayar Da Shayi A Kano

Kotun ta kuma tabbatar da hukuncin mai shari’a Joyce Abdulmalik, wanda ya hana shugabannin riƙon ƙwaryar ADC tsoma baki a harkokin shugabannin jihohin jam’iyyar da aka zaɓa bisa ƙa’ida.

Alƙalan kotun sun bayyana cewa ikon shirya taron zaɓen shugabannin jihohi yana hannun kwamitocin gudanarwa na jihohi da aka zaɓa, ba shugabancin ƙasa na jam’iyyar ba.

Sai dai shugaban kwamitin alƙalan, mai shari’a Abba Mohammed, ya yi saɓanin ra’ayi inda ya ce batun rikicin cikin gida ne na jam’iyya wanda bai kamata kotu ta shiga ba.

Advertisement

Tun da farko, babbar kotun tarayya ta yanke hukuncin cewa wa’adin shugabannin jihohin ADC na tsawon shekara huɗu ya na nan daram har sai an gudanar da sahihin tarukan zaɓe tare da babban taron ƙasa na jam’iyyar.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da wasu mambobin jam’iyyar ADC su ka shigar, su na ƙalubalantar matakin kwamitin riƙon ƙwarya na David Mark na kafa kwamitocin da za su gudanar da zaɓen shugabannin jihohi.

Kotun ta ce ta ɗauki wannan mataki ne domin kare demokaraɗiyya da hana rikici, ta na mai bayyana cewa duk lokacin da a ka gabatar da ƙorafi kan take kundin tsarin mulki, kotu na da ikon shiga tsakani.

Saboda haka, kotun ta yi watsi da ƙarar ɗaukaka ƙarar da jam’iyyar ADC ta shigar domin soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya.

Har ila yau, kotun ta bayyana cewa duk tarukan zaɓe da babban taron ƙasa da shugabancin David Mark ya gudanar ba su da inganci, domin an gudanar da su ne duk da umarnin kotu da ke hana hakan.

A ƙarshe, kotun ɗaukaka ƙara ta ci tarar jam’iyyar ADC kuɗi naira miliyan 10.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending