News
Zargin Ɓata Suna: Gbajabiamila Ya Kai Adeyemi Kotu, Ya Nemi Diya Ta Naira Biliyan 15.2
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan Frins Adeniyi Adeyemi Matthew, bisa zargin ɓata masa suna.
A cikin ƙarar, Gbajabiamila ya nemi kotu ta umarci Adeyemi ya biya shi diyyar Naira biliyan 15.2, yana mai cewa kalaman da ya yaɗa a kansa sun jawo masa zubewar mutunci da martaba.
Yan Bindiga Sun Tilastawa Mazauna Ƙauyukan Tserewa Daga Gidajensu A Benue
Ya ce zargin da aka yi masa na neman cin hanci ƙarya ce, kuma ba ta da wata hujja. Saboda haka, ya roƙi kotu ta tilasta wa wanda ake ƙara ya janye kalaman tare da bayar da uzuri a bainar jama’a.
Rahotanni sun nuna cewa Adeyemi, wanda ake zargi da bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na wata hukuma mai suna PFIPC, ya taɓa zargin Gbajabiamila da yunƙurin amfani da hukumomin tsaro a kansa. Haka kuma ya yi iƙirarin cewa marigayi Babatunde Tanimola ya kasance mai shiga tsakaninsu.
Sai dai Gbajabiamila ya musanta dukkan waɗannan zarge-zarge, yana mai cewa ƙirƙirarru ne kuma ba su da wani tushe.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, Adeyemi bai fito da wata sanarwa a hukumance ba game da ƙarar da aka shigar a kansa.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
