Uncategorized
DSS Ta Kama Jami’in Bogi Da Kayan Hukumar A Abuja
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama wani mutum, Moferewa Maiye, bisa zargin kwaikwayon jami’in hukumar da kuma amfani da kayan DSS wajen tsoratar da jama’a da karɓar kuɗi a Abuja.
An kama Maiye ne a maboyarsa da ke kusa da mahadar NITEL, kan titin Adetokunbo Ademola, Wuse II, Abuja, bayan jami’an hukumar sun samu bayanan sirri kan ayyukansa.
Bai Kamata A Kafurta Wanda Bai Zabi Muslim-Muslim Ba’ —Sheikh Daurawa
A lokacin da aka kama shi, jami’an DSS sun same shi sanye da kayan aiki irin na hukumar, tare da bindigar bogi.
Wata majiya daga ɓangaren tsaro ta ce wanda ake zargin ya kasance yana amfani da kayan hukumar da bindigar bogin wajen tsoratar da masu ababen hawa da sauran jama’a, tare da karɓar kuɗi daga hannunsu.
Majiyar ta ce yayin da ake yi masa tambayoyi, Maiye ya bayyana cewa ɗan’uwansa, Monday Maiye, wanda ya rasu shekaru da dama da suka gabata, ya kasance jami’in DSS.
A cewarsa, kayan hukumar da aka same shi da su na ɗan’uwansa ne da ya rasu.
A halin yanzu, DSS na ci gaba da yi wa wanda ake zargin tambayoyi, yayin da ake bincike kan yadda ya mallaki kayan hukumar da kuma tsawon lokacin da ya shafe yana kwaikwayon jami’an tsaro.
-
News5 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
News6 days ago
An Tura Kwamishinonin ’Yansanda 30 Da Jami’ai 15,000 Domin Sanya Ido A Zaɓen Osun
-
News3 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
