News
Jami’an Yansanda Sun Cafke likitoci Kan Zargin Safarar Mutane Da Cire Musu Ƙoda
Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta cafke wasu mutane huɗu, ciki har da likitocin ƙoda biyu, bisa zargin hannu a wata ƙungiyar safarar mutane da cire sassan jikin bil’adama ba bisa ƙa’ida ba a Jihar Nasarawa.
Waɗanda aka cafke sun haɗa da Emmanuel Ode, mai shekaru 23; Dakta Benjamin Oyime, mai shekaru 48, likitan ƙoda kuma mai ba da shawara a Asibitin Wellington da ke Life Camp, Abuja; Dakta Daniel Otukpa, mai shekaru 53, shi ma likitan ƙoda kuma Mukaddashin Daraktan Ayyukan Kula da Lafiya na asibitin; da David Idoko, mai shekaru 25.
KADUNA: Jami’an Ƴansanda Sun Tarwatsa Sansanonin Ƴan Bindiga A Makarfi
Jami’an Special Tactical Squad (STS) ne suka kama mutanen a ranar 19 ga Agustan 2026, yayin wani samame da suka gudanar a Auta Balifi, cikin Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa, bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ƙungiyar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Ani Iniedu, ya ce binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun mayar da hankali ne kan matasa masu rauni da kuma waɗanda ke fama da matsalar kuɗi a Nasarawa da kewaye.
A cewar ’yan sandan, Ode ya amsa cewa yana ɗaukar waɗanda abin ya shafa ne ta hanyar yaudararsu. Rundunar ta ce a ranar 24 ga Afrilun 2026, ya kai wani matashi mai suna Samuel Ezekiel, mai shekaru 22, zuwa Asibitin Wellington da ke Abuja, inda ake zargin an cire masa ƙoda tare da biyan sa dala 1,250, wato kusan Naira miliyan 1.7.
Rundunar ta ce wani mutum na biyu da ake zargin ya shaida cewa Ode ne ya yaudare shi a shekarar 2022 zuwa wani asibiti, inda aka cire masa ƙoda sannan aka biya shi Naira miliyan bakwai.
’Yan sandan sun kuma ce bincike ya gano cewa ana amfani da takardun bogi, ciki har da NIN, takardun haihuwa, takardun bayyana shekaru, takardun rantsuwa da kuma takardun amincewa, domin sauƙaƙa aikata laifukan.
Rundunar ta ce an ƙwato wasu kayayyaki da ake zargin an saya da kuɗin da aka samu daga aikata laifin, yayin da bincike ke ci gaba da gudana domin cafke wasu mutane da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyar.
-
News3 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
-
News4 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
