Connect with us

News

Gwamnan Plateau Ya Hana Ayyukan HISBA A Jos

Published

on

1788132611689

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya umarci jami’an tsaro da su dakatar da ayyukan wata ƙungiya mai suna HISBA, wadda ake zargin tana gudanar da ayyukanta a wasu sassan Ƙaramar Hukumar Jos North.

Gwamnan ya bayyana ayyukan ƙungiyar a matsayin waɗanda ba su da izini kuma suka saɓa wa doka, tare da umartar jami’an tsaro da su gudanar da bincike kan mutanen da ke da hannu a ayyukan.

Jami’an Ƴansanda Sun Kama Mutune 17 Bisa Zargin Aikata Laifuka Daban-daban A Jigawa

Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na gwamnan, Dr Gyang Bere, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce matakin ya biyo bayan rahotannin da ke zargin ƙungiyar da tsoratar da mazauna yankin, cin zarafinsu, karɓar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba, da kuma kafa dokoki da takunkuman da ba su da tushe a doka.

Mutfwang ya gargadi mutanen da ke da hannu a ayyukan da su dakata nan take, ko kuma su fuskanci kama da gurfanar da su a gaban kotu.

Advertisement

Ya ce Plateau tana da Kundin Tsarin Mulki guda, tsarin doka guda da kuma halastacciyar hukuma guda, don haka babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon ɗaukar nauyin gwamnati ko tilasta wa jama’a bin wasu dokoki ba tare da izinin doka ba.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending