Connect with us

News

Zaben 2023: Gwamna Ganduje ya umarci duk masu neman mukaman siyasa da su yi murabus.

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

 

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya umurci duk masu rike da mukaman siyasa da ke neman mukaman siyasa a zabe mai zuwa na 2023 da su yi murabus daga mukamansu.

Wannan dai na ƙunshe cikin wata sanarwar da
babban sakataren yada labarai na gwamnan Jihar Kano Abba Ansar ya fitar a yau Asabar, inda ya ce “an baiwa masu riƙe da mukaman daga yanzu zuwa Litinin 18 ga Afrilu, 2022, da su yi murabus.”

Advertisement

Domin bin sashe na 84 (12) na sabuwar dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima.

Sashen dai na 84 (12) na sabuwar dokar zaben, ya bukaci duk wani mai rike da mukamin gwamnati, a kowani mataki, da ya ke da sha’awar yin takara a zaɓen ƙasar nan, da ya sauka daga mukaminsa.

Gwamna Ganduje dai ya bi sauran takwarorin sa na sauran jihohi wajen bada irin wannan umarnin.

Rahotanni na cewa wasu daga cikin masu riƙe da mukaman a cikin gwamnatin ba’a shirin fitowa takara domin fafatawa da su a zaben mai zuwa a matakai daban daban ciki har da takarar gwamna, sanatoci da kuma yan majalisu.

Sai dai har yanzu babu wanda ya fito ya bayyana aniyar ta sa a fili.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending