Connect with us

Labarai

Mota Ta Afka Ma’ajiyar Tukwanan Gas A Abuja

Published

on

Kubwa explosion 768x539 (1)
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Wata mota ta afka cikin wata ma’ajiyar tukwanen iskar gas da ke yankin Arab Road, Kubwa, a Abuja, a safiyar Lahadi, lamarin da ya haddasa fashewar wasu daga cikin tukwanen gas.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:15 na safe, inda fashewar ta jefa mazauna yankin cikin firgici.

Mota Ta Afka Ma’ajiyar Tukwanyar Gas A Abuja

Shaidu sun ce ƙarar fashewar ta kasance mai ƙarfi, inda aka iya jin ta daga nisan kilomita da dama daga wurin da lamarin ya faru.

Wasu mazauna Rukunin Gidajen Ɗantata da ke Kubwa, wanda ke da nisan kusan kilomita biyu daga wurin, sun ce tasirin fashewar ya sa gine-gine suka girgiza.

Fashewar ta kuma lalata wani shinge da allunan alama da ke Liberty Junction, yayin da gobara ta kama wasu shaguna da ke kusa da ma’ajiyar.

Advertisement

Motar da ta afka cikin ma’ajiyar ta ƙone ƙurmus, sai dai an samu nasarar ceto direban motar da wani yaro da ke cikinta, inda aka garzaya da su asibiti domin samun kulawar gaggawa.

Jami’an kashe gobara da sauran hukumomin tsaro sun isa wurin domin shawo kan gobarar da kuma tabbatar da tsaron jama’a. Haka kuma, jama’a sun yi cincirindo a wajen, lamarin da ya haddasa cunkoso a kan hanya yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da ayyukansu.

 

 

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending