Labarai
Dakarun Soji Sun Kubutar Da Matafiya 41 Daga Hannun Yanbindiga A Zamfara

Sojoji da ke aiki ƙarƙashin rundunar Fansan Yamma sun kuɓutar da matafiya 41 da ƴanbindiga suka sace bayan da motarsu ta lalace a kan wata babbar hanya da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
A cewar wata sanarwa da muƙaddashin daraktan yaɗa labarai na rundunar, Leftanar Kanar Olaniyi Osoba, motar ta taso ne daga Senegal zuwa jihar Kano a lokacin da ta samu matsala.
“Bayanai na cewa ƴanbindigar sun yi amfani da matsalar da fasinjojin suka shiga ta lalacewar mota don far musu da kuma yunƙurin yin garkuwa da su.”
Sojojin sun samu bayanan sirri kuma nan take suka garzaya zuwa wajen inda kuma aka yi arangama tsakaninsu.
Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin sun tilasta wa ƴanbindigar tserewa cikin gonaki inda kuma suka bar fasinjojin.
Laftanar Kanar Olaniyi ya ce an kuɓutar da duka fasinjojin 41 da suka haɗa da maza 24 da mata 10 sai yara 7 kuma babu wanda ya ji rauni sannan a cewarsa suna samun kulawar da ta dace a wajen sojojin..
