Connect with us

News

Akwai yiwuwar akai hare-haren bam da karamar sallah – ‘Yan sandan Najeriya

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fitar da wata sanarwa cewa akwai yiwuwar wasu miyagu su kai hare-haren bam kan al’umma yayin karamar sallah mai zuwa wadda ta kawo karshen watan Azumin Ramadan.

Advertisements
Advertisements

Cikin sanarwar, kakakin Rundunar Peter Afunanya ya ce an gano wani shirin da wasu kungiyoyi suka kitsa domin kai hare-haren kan wasu mhimman wurare da masallatai da kuma wuraren shakatawa.

Wannan gargadin na zuwa ne bayan da wasu abubuwa suka fashe a mashaya a jihohin arewa maso gabashin Najeriya biyu – Yobe da taraba – inda mutane da dama suka halaka.

Wani tsagin kngiyar Boko Haram da aka fi sani da ISWAP ne ta dauki alhakin kai hare-haren.

Advertisements
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending