News
Nijar ta hana fitar da man da aka tace a ƙasar zuwa ƙasashen waje
Daga kabiru basiru fulatan
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da aka tace, kamar yadda gwamnatin kasar ta bayyana a cikn wata sanarwa a ranar Laraba, a wani mataki na tabbatar da wadatuwar man a ƙasar.
Majalisar dokoki ta dakatar da ciyamomin Ƙananan Hukumomi 2 a Kaduna
Tun a farkon watan Mayu Nijar ta rage yawan man da take fitarwa da kashi 75 domin ƙara yawaitar man a cikin ƙasa yayin da farashn ɗanyen mai ke ƙara tsada a kasuwar duniya wanda yaƙin Ukraine ya haddasa.
Ma’aikatar kula da cinikayya da albarkatun man fetir ta ƙasar ta ce matakin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Yuni.
Nijar na cikin sabbin ƙasashen Afirka da ke tace mansu domin amfann ƴan ƙasa a ƙaramar matatar mai da ke tace ganga 20,000 a rana.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
