Connect with us

News

Fashewa a ma’adanar fetur ta kashe mutum 32 a Bangladesh

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Wata fashewa mai girma a kusa da birnin Chittagong na ƙasar Bangladesh ta kashe akalla mutum 32.

Advertisement

An bayar da rahoton cewa ɗaruruwan mutane ne suka jikkata sakamakon fashewar, wadda ta faru a bayan wata ma’ajiyar man fetur da ke Sitakunda.

Hukumomi sun ce ma’aikatan kashe gobara na cikin wadanda suka mutu.

Advertisement

Wakiliyar BBC ta ce asibitoci a yankin sun cika maƙil suna neman a ba su gudummawar jini, sannan mahukunta na gargaɗin cewa ana sa ran adadin wadanda suka mutu zai karu.

NAHCON ta sanar da farashin aikin Hajjin bana

Advertisement

Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin tashin gobarar ba amma ana tunanin an ajiye sinadarai ne a cikin wasu daga cikin kwantenonin da ke wurin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending