Connect with us

News

Ni Zan Daidaita Duk Abinda APC Ta Lalata A Nijeriya—Kwankwaso

Published

on

Rabi’u Musa Kwankwaso,

Daga kabiru basiru fulatan 

 

 

 

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin magance matsalar rashin tsaro, samar da ingantaccen ilimi a kasar Nijeriya idan ya zama shugaban kasa.

Advertisement

Ƴan Boko Haram sun ɗauke mata 2 a Monduga — Kwamishinan Ƴan Sanda

Tsohon ministan tsaro kuma gwamnan jihar Kano, ya kuma ce zai bullo da kyawawan manufofin tattalin arziki da za su ciyar da kasar gaba.

 

Jam’iyyar LP Ta Obi Na Shirin Kulla Auren Siyasa Da NNPP Ta Kwankwaso —Dakta Tanko

Kwankwaso ya yi wannan alkawarin ne a ranar Litinin yayin da yake gabatar da jawabi a cibiyar ‘yan goro dake Calabar, a wata ganawa da wakilan jam’iyyar NNPP a Calabar.

 

Advertisement

Ya bayyana cewa, in ya lashe zaben, rashin tsaro da ya addabi al’ummar kasar nan a ‘yan kwanakin nan, zai zama tarihi da yardar Allah.

 

Ya ba da tabbacin samar da ingantaccen ilimi da ingantattun tsare-tsare na tattalin arziki da za su taimaka wajen juya arzikin kasa, inda ya yi kira ga ‘yan Nijeriya na gida da na kasashen waje da su hada kai wajen zaben sa a matsayin shugaban kasa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending