Connect with us

News

Ikweremadu: Kotu ta amince wanda zai ba da gudunmawar ƙoda ba yaro ba ne

Published

on

Daga kabiru basiru Fulatan

 

 

Advertisement

 

Ɗan Majalisar Dattawan Najeriya Ike Ekweremadu da matarsa ​​sun sake gurfana a gaban kotu a London, bisa zarginsu da hada baki wajen kai wani mutum kasar Birtaniya domin bayar da gudummawar wasu sassan jikinsa.

Advertisement

Alkalin kotun ya amince da cewa wanda ya shigar da karar ba yaro bane kamar yadda aka ruwaito a baya.

Ƴan fansho sun yi zanga-zanga a Taraba

Advertisement

Beatrice mai shekaru 56 ta bayyana a gaban kotun sanye da bakar riga ƴar ciki, da fara mai duhu a sama.

Shi kuwa mijinta Ike mai shekaru 60 ya bayyana ne sanye da ƙananan kaya da tabarau a idonsa.

Advertisement

An zaunar da wani jami’in gidan kason da suke a tsakanin sanatan da matarsa.

Mataimakin Babban Alkalin Kotun Tan Ikram ne ya jagoranci zaman na tsawon mintuna 20, wanda ya aike da karar zuwa Old Bailey domin sauraren karar ranar 4 ga watan Agusta.

Advertisement

Wajen ya cika da magya baya da ƴan uwa da abokan arzikin Sanatan da suke je don ƙara masa ƙwarin guiwa.

Yanzu dai zai ci gaba da kasancewa a gidan yari, kafin ranar 5 ga wata mai zuwa da za a ci gaba da sauraron ƙarar a kotun Old Bailey.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending