Ɗumbin ƴan fansho sun gudanar da zanga-zanga a gidan gwamnatin jihar Taraba da ke Jalingo, saboda kin biyansu hakkokinsu.
Sun fito ne daga dukkan ƙananan hukumomin jihar bisa rakiyar ƴaƴansu da matansu.
Hadarin mota ya kashe mutum tara a kan hanyar Kaduna-Zaria
Tun da farko sun fara taruwa ne a shalkwatar kuniyarsu ta jihar daga bisani suka dunguma suka nufi fadar gwamnatin jihar suna rera wakokin neman a biya su haƙƙokin na su.
