Connect with us

News

Hadarin mota ya kashe mutum tara a kan hanyar Kaduna-Zaria

Published

on

Daga kabiru basiru fulatan

 

MutuM tara sun mutu, yayin da wasu sha biyu suka jikkata a wani hadarin mota tsakanin ababen hawa guda hudu a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria da ke arewacin Najeriya.

Advertisement

Zargin Batanci: Lauyan Abduljabbar Ya Fice Daga Kotu A Fusace

Kwamandan hukumar kiyaye hadura ta kasa, reshen jihar Kaduna, Hafiz Mohammed, shi ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a yau Alhamis.

Advertisement

A cewarsa, hadarin ya faru ne da misalin karfe biyar na safiya a kan gadar Rigachikun kusa da Jami’ar karatu daga gida NOUN, inda direbobin tirela biyu da direban bas da kuma Toyota suka yi taho mu-gama.

Mohammed ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa mutum tara suka mutu yayin da sha biyu kuma suka sami munanan raunuka, inda aka garzaya da su zuwa asibiti domin yi musu magani.

Advertisement

Ya dora laifin hadarin kan gudu fiye da kima da kuma rashin bin dokokin hanya.

Yanzu dai an kai gawarwaki da lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin Koyarwa na Barau Dikko da kuma asibitin St. Gerrard da ke Kaduna.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending