Connect with us

News

Iran na shirin bai wa Rasha jirage marasa matuka – Amurka

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Jami’an a Amiurka sun ce hukumomin Iran na yunkurin tallafa wa Rasha da jirage marasa matuka wadanda ke iya harba makamai a yakin da take yi a Ukraine.

Advertisement

Babban mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokokin tsaro Jake Sullivan, ya ce bayanan da suke samu na nuna cewa Iran na shirin bai wa dakarun Rasha horo kan yadda ake aiki da jiragen.

Ya kara da cewa kawo yanzu ba su da masaniya, ko Iran din ta riga ta miƙa makaman ga kasar ta Rasha.

Advertisement

Duka kasashen biyu na amfani da jiragen marasa matuka a yakin da suke tsakaninsu.

A makon da ya gabata ne dai Ukraine ta yi kira ga kasashen duniya da su taimaka mata da dubban irin wadannan jirage domin kara karfiin dakarunta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending