News
Ba guba ce ta kashe tsohon shugaban Angola ba – Bincike
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Babbab lauyan gwamnatin Angola ya ce sakamakon binciken musabbabin mutuwa da aka yi wa gawar tsahon shugaban kasar ya nuna cewa ba guba ce ta kasahe shi ba, kamar yadda ‘yarsa ta yi zargi.
Wata kotu ce a birnin Barcelona na kasar Spain ta bayar da umarnin gudanar da binciken bayan da ‘yar marigayin Tchize dos Santos ta nemi kotun da ta yi hakan, bayan ta yi zargin cewa kashe mahaifin nata aka yi.
Mista Dos Santos dai ya mutu a wani asibiti da aka kwantar da shi a birnin Barcelona ranar Juma’ar da ta gabata.
Iyalai da lauyoyin mamacin sun yi watsi da kiran da shugaban Angola ya yi na cewa a mai do gawar marigayin kasar domin yi mata jana’izar ban girma a kasa.
Inda suka ce a maimakon haka za a binne gawar Dos Santos a kasar Spain.
