News
Al’umma a yawaita addu’a don samun zaman lafiya….Kwamared Hafiz Mustapha
Daga yasir sani Abdullah
Dan takarar majalisar dokokin Kano a karamar hukumar Gwarzo, Kwamared Hafiz Mustapha yayi kira ga al’umma dasu cigaba da yiwa kasar nan addu’a don samun zaman lafiya mai dorewa.
Kada a gajiya wajen yin addu’a don samun zaman lafiya-Hamisu Ibrahim chadari.
Hafiz Mustapha, wanda ke takara karkashin jam’iyar PRP yayi wannan kirane a sakon barka da sallah wanda mai taimakamasa na musamman kan kafofin yada labarai Aminu Abdullahi Ibrahim ya fitar a ranar Asabar.
Ya ce za samu saukin matsalar tsaron da kasar nan take ciki ne kawai ta hanyar addu’a tare da mika lamura ga Allah madaukakin sarki.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Gwarzo da Getso dasu yi rijistar katin zabe domin kada kuri’un su a zaben 2023 dake tafe.
Kwamared Hafiz Mustapha, ya kuma ce ba zai baiwa al’ummar Gwarzo da Getso, kunya ba matukar suka zabe shi amatsayin dan majalisa dokokin jihar Kano.
Ya kuma yi fatan al’ummar jihar Kano zasu cigaba da shagulgulan sallah lafiya.
-
News7 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News7 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
