Connect with us

News

Zaman Lafiya Zai Dawo Najeriya Kafin Buhari Ya Bar Mulki A Shekarar 2023- Abubakar Malami

Published

on

Abubakar Malami

Daga kabiru basiru fulatan

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Gwamnati, Abubakar Malami, ya ba da tabbacin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai dawo da Najeriya kan tafarkin zaman lafiya kafin ya bar mulki a 2023.

Advertisement

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Birnin Kebbi, domin taya Musulmi murnar Sallar Layya.

Kada a gajiya wajen yin addu’a don samun zaman lafiya-Hamisu Ibrahim chadari.

Advertisement

Malami ya ce sam Buhari ba ya barci, ba wai kawai don ganin ya mika mulki cikin ruwan sanyi ba, yana ma kokarin ganin ya kawo karshen matsalar tsaron da ke addabar kasar.

Ya ce, “Ina so in tabbatar muku da cewa gwamnatin Buhari za ta ci gaba da yin dukkan abin da ya kamata wajen dawo da tsaro a Najeriya.

Advertisement

“Muna addu’ar Allah ya amsa addu’o’inmu, ya dawo da zaman lafiya a Jihar Kebbi da ma kasa baki daya, da kuma tabbatar da mika mulki cikin ruwan sanyi a badi,” inji Malami.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ce dai wa’adin Buhari zai kare na shugabancin Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending