Uncategorized
Ba na sa ran ƴan ƙasa za su yaba min bayan na bar mulki — Buhari
Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya ce shi dama ba ya sa ran ƴan Nijeriya za su yaba masa bayan ya bar mulki.
Buhari ya baiyana hakan ne a hira ta musamman da ya yi da gidan talabijin na ƙasa, NTA.
Buhari ya ce shekara da shekaru ya na riƙe madafun iko a ɓangarori daban-daban a ƙasar nan kuma ya bada iya gudunmawar da zai iya bayarwa ga ƙasar.
“Me zan yi sama da abinda na yi wa ƙasar nan?”
Ya ƙara da cewa ya na fatan idan ya kammala mulkin sa a 2023, ƴan Nijeriya za su gane cewa ya yi iya iyawar sa.
“Na yi gwamna, na yi minista kuma gani a karo na biyu a matsayin shugaban ƙasa. Sabo da haka an dama da ni a harkar mulki. To, me kuka zan yi sama da wannan?,” In ji Buhari.
“Ni yi iya kokari na kuma ina fatan bayan na bar mulki, ƴan Nijeriya za su yi duba na tsanaki. Ni ba na tsammanin wani yabo, amma abin da na ke tsammani shine ƴan Nijeriya za su ce mutumin nan ya yi iyakar ƙoƙarin sa. Ni wannan na ke tsammani da ga ƴan Nijeriya,” in ji Buhari.