News
Babban Taron APC na Ƙasa: Gwamnoni sun nemi Buni da ya ajiye shugabancin jam’iya
Daga kabiru basiru fulatan
Muryar Gwamnonin APC, PGF, ta yi kira ga Shugaban Jam’iya na Riƙon Ƙwarya, Mai Mala Buni da ya ajiye nukamin sa idan har ba zai kira Babban Taron Jam’iya na Ƙasa a watan Febrairu ba.
Darakta-Janar na PGF, Lukman Salihu ne yai wannan kiran a wata wasiƙa da ya sanyawa hannu a ranar 5 ga watan Janairu.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa Salihu ya ce jam’iyar APC na cikin mawuyacin hali, inda ya ƙara da cewa “duk wani yunƙuri na ƙara ɗaga ranar yin Babban Taron Jam’iya na Ƙasa to ya nuna cewa a na wasarere da makomar jam’iyar.”
“Maganganun da su ke fitowa a ciki jam’iyar shine cewa Buni ya na jan kafa wajen yin babban taron domin gwamnonin jihohi na son su ci gaba da juya jam’iyar a Jihohin su.
“Ya kamata manyan jam’iya su kira ganawa ta gaggawa sai a tambayi Buni da sakataren jami’ya, John Akpanudoedehe, a ji menene matsalar kuma wacce barazana su ke fuskanta,” in ji Salihu.
A ƙarshe, Salihu ya ƙalubalanci Buni, wanda shine Gwamnan Jihar Yobe da ya gabatarwa Shugaban Ƙasa kundin rijistar yan jam’iya, inda ya nanata cewa jam’iyar na cikin mawuyacin hali.