Sports
Kalaman Bruno kan alakanta shi da komawa Barcelona
Daga usman Abdullahi jibirin Nguru Yobe
Dan wasan tsakiya na Manchester United, Bruno Fernandes ya mayar da martani kan rade-radin da ake alakanta shi da komawa Barcelona.
Fernandes ya yi watsi da jita-jita yayin da ya zama dan wasan Manchester United na baya-bayan nan da ya karyata rahotannin rashin jin dadi a sansanin Manchester United.
Dan wasan tsakiyar ya ji daɗin kaka biyu masu kyau tare da Manchester United amma ta uku ta zo masa da wahala.
Dan wasan na Portugal ya ci kwallo daya kacal a wasanni 14 na karshe da ya yi a gasar Premier bana.
An samu rahotannin mummunan jini a tsakanin ‘yan wasa a Old Trafford sakamakon jerin munanan sakamako, ciki har da rashin nasara a hannun Wolves na baya-bayan nan a Old Trafford.
Tashar talabijin ta SPORT ta Portugal ta rawaito cewa an yi tayin dan wasan tsakiyar Portugal Fernandes ga Barcelona.
Amma dan wasan mai shekaru 27 ya karyata jita-jitar ta salo mai ban sha’awa, inda ya kwatanta ta da barkwancin ne kawai.
Da yake mayar da martani ga sakon SPORT TV a Instagram, ya amsa da cewa: “Kuma ina tsammanin sabuwar shekara ta fara ne kwanaki kadan da suka gabata, amma mun riga mun kasance ranar 1 ga Afrilu! Ko kuwa wannan aikin jarida mara kyau ne kawai” in ji Fernandez.