Connect with us

Sports

Afcon 2021: Kamaru za ta fara wasa da Burkina Faso a Yaounde

Published

on

FB IMG 16417291777275235
Spread the love

Daga muhammad muhammad zahraddin

Kamaru za ta fara wasa da Burkina Faso ranar Lahadi a gasar cin kofin nahiyar Afirka da take karbar bakuncin gasar bana.

Wasannin rukunin farko

Advertisement

Lahadi 9 ga watan Janairu: Kamaru da Burkina Faso, Habasha da Cape Verde

Alhamis 13 ga watan Janairu: Kamaru da Habasha, Cape Verde da Burkina Faso

Litinin 17 ga watan Janairu: Burkina Faso da Habasha, Cape Verde da Kamaru

Advertisement

Tun cikin watan Yunin 2019 ya kamata Kamaru ta karbi bakuncin babbar gasar tamaula ta Afirka, amma aka dage wasannin saboda yanayi da yake lokacin damuna ne a kasar, sannan cutar korona ta kai tsaiko.

Saboda haka hukumar kwallon kafar Afirka ta tsayar da ranar 9 ga watan Janairu domin fara wasannin bana.

Yanzu dai ta tabbata cewar Kamaru za ta fara wasa da Burkina Faso a gasa ta 33 a wasannin cin kofin Afirka da za su kece raini a sabuwar sitadiya da ke Olembe.

Advertisement

Wasan farko

Rana: 9 ga watan Janairu 2022

Lokaci17:00 agogon Kamaru (16:00 GMT)

Advertisement

Wurin wasanOlembe Stadium, Yaounde

Karawar rukunin farko

Mai masaukin baki Kamaru da ake kira Indomitable Lions mai rike da kofi biyar na fatan fara gasar bana da kafar dama da ya ke za ta samu dunbin magoya baya da za su kara mata kwarin gwiwa a wasanninta.

Advertisement

Kamaru wadda ta dauki lokaci tana ta shirye-shiryen yadda za ta gudanar da gasar nan, haka kuma a bangare daya tana sa ran lashe kofin da take karbar bakunci kuma a karon farko a gida.

Yanzu shekara 50 da kasar ta karbi bakuncin wasannin da aka yi a 1972, saboda haka dama ce a wajenta ta kafa tarihin daukar kofin a gida, kuma na shida jumulla, bayan da Masar ce kan gaba a yawan daga kofin mai bakwai a tarihi.

Burkina Faso

Advertisement

Burkina Faso ta je Kamaru ne da zummar taka rawar gani da yin abin kirki da zai dara lokacin da ta kai wasan karshe a 2013 da ta yi rashin nasara a hannun Najeria da ci 1-0.

Sai dai kuma fuskantar mai masaukin baki abu ne mai tattare da kalubale, amma duk da hakan, Burkina Faso tana sa ran za ta iya lashe kofin bana.

Sau nawa suka kara a tsakaninsu?

Advertisement

Wannan shine karo na uku da za a fafata tsakanin Kamaru da Burkina Faso a Afcon.

Kuma dukkan wasa biyun sun hadu ne a fafatawar cikin rukuni, Inda Kamaru ta yi nasarar cin 1-0 a 1998, sannan suka tashi 1-1 a 2017.

Karo na 20 kenan da Kamaru za ta fafata a babbar gasar tamaula ta Afirka, wadanda ke gabanta a yawan zuwa wasannin sun hada da Masar mai 25 da Ivory Coast mai 24 da kuma Ghana da za ta buga gasa ta 23.

Advertisement

Wannan shine karo na 12 da Burkina Faso za ta barje gumi a Afcon, kuma a zuwa 11 da ta yi a baya an fitar da ita a karawar rukuni sau takwas da biyu a wasan daf da karshe da kuma rashin nasara a karawar karshe da Najeriya ta yi nasara da ci 1-0 a 2013.

Dan wasan Kamaru Vincent Aboubakar ya ci kwallo daya a wasa takwas a Afcon da kai hare-hare zuwa raga sau 18.

Sai dai kuma dan wasan ne ya ci wa Kamaru kwallo na biyu da ta yi nasara a kan Masar a wasan karshe da ci 2-1 da ta lashe kofin a 2017 a Gabon, kuma kwallon da ya zura a raga kenan

Advertisement

YAN WASAN KAMARU

Masu tsaron raga: Simon Omossola (AS Vita Club, DR Congo), Devis Epassy (OFI Crete, Greece), Andre Onana (Ajax, Netherlands).

Masu tsaron baya: Collins Fai (Standard Liege, Belgium), Olivier Mbaizo (Philadelphia Union, USA), Michael Ngadeu-Ngadjui (Gent, Belgium), JC Castelletto (Nantes, France), Harold Moukoudi (St Etienne, France), Enzo Ebosse (Angers, France), Ambroise Oyongo Bitolo (Montpellier, France), Jerome Onguene (Red Bull Salzburg, Austria), Nouhou Tolo (Seattle Sounders, USA).

Advertisement

Masu buga tsakiya: Jean Onana Junior (Bordeaux, France), Malong Kunde (Olympiakos, Greece), Andre-Frank Zambo Anguissa (Napoli, Italy), Samuel Gouet Oum (Mechelen, Belgium), Martin Hongla (Hellas Verona, Italy), James Lea Siliki (Middlesbrough, England), Yvan Neyou (St Etienne, France).

Masu cin kwallo: Ignatius Ganago (Lens, France), Christian Bassogog (Shanghai Shenua, China), Eric Maxim Choupo-Moting (Bayern Munich, Germany), Stephane Bahoken (Angers, France), Karl Toko-Ekambi (Lyon, France), Moumi Ngamaleu (Young Boys, Switzerland), Vincent Aboubakar (Al Nasr, Saudi Arabia), Clinton Njie (Dinamo Moscow, Russia).

‘YAN WASAN BURKINA FASO

Advertisement

Masu tsaron baya: Herve Koffi (Charleroi, Belgium), Aboubacar Sawadogo (Kadiogo, Burkina Faso), Soufiane Farid Ouedraogo (Fuenlabrada, Spain), Kilian Nikiema (ADO Den Haag, Netherlands).

Masu tsaron baya: Edmond Tapsoba (Bayer Leverkusen, Germany), Issoufou Dayo (Renaissance Berkane, Morocco), Steeve Yago (Aris Limassol, Cyprus), Oula Traore (Horoya, Guinea), Patrick Malo (Hassania Agadir, Morocco), Issa Kabore (Troyes, France), Hermann Nikiema (Salitas, Burkina Faso), Soumaila Ouattara (FUS Rabat, Morocco).

Masu wasan tsakiya: Adama Guira (Racing Rioja, Spain), Blati Toure (Eskilstuna, Sweden), Gustavo Sangare (Quevilly-Rouen, France), Ismahila Ouedraogo (PAOK, Greece), Dramane Nikiema (Horoya, Guinea), Saidou Simpore (Al Ittihad, Egypt), Eric Traore (Pyramids, Egypt), Cyrille Barros Bayala (AC Ajaccio, France), Hassane Bande (Istra 1961, Croatia).

Advertisement

Masu cin kwallo: Dango Ouattara (Lorient, France), Cheick Djibril Ouattara (Olympique Safi, Morocco), Zakaria Sanogo (Ararat-Armenia, Armenia), Kouame Botue (AC Ajaccio, France), Bertrand Traore (Aston Villa, England), Abdoul Tapsoba (Standard Liege, Belgium), Mohamed Konate (Akhmat, Russia).

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *