Connect with us

Sports

Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Ndombele, Bergwijn, Mbappe, Digne, Schick, Wood

Published

on

PSG Mabappe
Spread the love

 

Daga Yasir sani Abdullah

 

Advertisement

 

Dan wasan tsakiya na Faransa da Tottenham Hotspur Tanguy Ndombele mai shekara 25 na fatan komawa wata ƙungiyar cikin wannan watan . (The Athletic – subscription required)

Steven Bergwijn, dan wasan gefe ma na shirin rabuwa da Spurs, bayn da Ajax Amsterdam ta bayyana sha’awar dan wasan mai shekara 24. (Fabrizio Romano on Twitter)

Advertisement

Shi kuwa ɗan wasan gaba na Paris St-Germain Kylian Mbappe mai shekara 23 na iya sauya ra’ayinsa na komawa Real Madrid, inda aka ce yana iya sanya hannu a sabuwar kwantiragi da PSG. (Le Parisien – in French)

Dan wasan gaba na Bayer Leverkusen da kasar Czech Patrick Schick mai shekara 25 ya ce ba ya sha’awar barin ƙungiyarsa duk da maganganun da ake yi cewa zai sauya sheƙa a wannan watan na Janairu. (Bild – in German)
Aston Villa ta yi nisa a tattaunawar da ta ke yi domin dauko dan wasan baya mai shekara 28 Lucas Digne daga Everton domin yana sha’awar komawa wajen kungiyar Steven Gerrard. (Sky Sports)

Newcastle United ta tuntubi Burnley domin ɗauko ɗan wasan gaba na ƙasar New Zealand Chris Wood, mai shekara 30. (Telegraph – subscription required)

Advertisement

Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya yi shaguɓe cewa dan wasan tsakiya na Ingila Ross Barkley mai shekara 28 na iya komawa wata ƙungiyar a wannan watan a matsayin ɗan aro. (90 Min)

Ɗan wasan tsakiya na Manchester City Tommy Doyle ya kammala wa’adinsa tare da Hamburg, inda dan wasan mai shekara 20 ke shirin sake tafiya wata kungiyar daga Etihad cikin wannan watan. (Manchester Evening News)

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *