News
Bola Tinubu: Tsohon gwamnan Legas ya shaida wa Buhari zai yi takarar shugaban ƙasa a 2023
Daga muhammad muhammad zahraddin
Tsohon gwamnan Legas, kuma jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya ce ya faɗa wa shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasar a zaɓen 2023.
Ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Litinin.
A cewar Tinubu “na faɗa wa Shugaba Buhari aniyata, ban ji abun da ba shi na yi tsammanin ji daga gare shi ba, ya ƙarfafa min guiwa kamar yadda dumokuraɗiyya ta ba ni dama, amma har yanzu ban sanar da jama’ar Najeriya ba tukunna, ina ci gaba da tuntuɓa.”
“Tuntuni nake fatan zama shugaban ƙasa a tsawon rayuwata, don haka me ya sa zan yi tsammanin jin abun da ya saɓa da wannan daga wajen shi, tsari muke yi da dimokuraɗiyya, don haka dole mu tafi a kan haka”, in ji shi.
Tun a bara ne hotunan takarar Tinubu suka fara karaɗe wasu jihohin Najeriya, ko da yake ya ja bakinsa ya yi gum, in ban da a yanzu da ya sanar da shugaba Buhari wannan fata baki da baki.
Masu lura da lamuran siyasa suna gani Tinubu zai fuskanci ƙalubale wajen samun tikitin yi wa APC takarar shugaban ƙasa a 2023, musamman ganin yadda shekarunsa suka ja kuma ‘yan kasar na fatan ganin an zabi mai jini a jika. Sai dai wasu ƴaƴan jam’iyyar na ganin ya kamata a saka masa da wannan takara ko don irin wahalar da ya yi wa APC da shugaba Muhammadu Buhari a zaɓukan 2015-2019.
Ko da yake Tinubu ne mutum na farko da ya furta cewa zai yi takara zuwa yanzu, akwai wasu fjiga-jigai a jam’iyyar waɗanda su ma ake kyautata zaton za su yi takara, ciki har da mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo wanda tuni wasu ƙungiyoyi suka fara yi masa kamfe.
Haka kuma akwai gwamnonin da ake ganin za su fito takarar shugaban kasar.
Akwai kyakkyawan zaton cewa APC za ta miƙa wa yankin kudu maso yamamcin Najeriya takarar shugaban ƙasa a 2023, don haka ake ganin cewa Tinubu wanda uban gidan Osibanjo ne a siyasance, a wannan karon zai ɓarje gumi da yaronsa na siyasa wato Osinbajo waɗanda dukkansu daga yankin suka fito.
Wasu mutane dai na ƙishin-ƙishin ɗin cewa ba lallai ne wasu gwamnonin jam’iyyar ta APC musamman a arewacin ƙasar su goyi bayan Tinubu ba, yayin da wasu na ganin cewa ya yi kafuwar da ture shi a jam’iyyar sai an shirya.