News
Tinubu ya gana da Buhari, ya kuma ce ‘ba ni da burin da ya wuce in zama Shugaban Ƙasa’
Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da Jagoran Jami’yar APC na Ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Kamfanin Daillancin Labarai na ƙasa, NAN, ya baiyana cewa kawo yanzu, ba san me shugabannin su ka tattauna ba.
Amma wasu majiyoyin sun ce Tinubu ya ziyarci shugaban ƙasa me domin taya shi murnar sabuwar shekara da kuma tattauna wasu muhimman batutuwa.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Tinubu na da burin tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023.
Da a ka tambaye shi ko ya sanarwa shugaban ƙasar aniyar sa ta tsayawa takara, sai kuwa Tinubu ya tabbatar da hakan.
“Na dai fadawa shugaban ƙasa aniya ta amma har yanzu ban shaidawa ƴan ƙasa , ina dai tuntuɓa a kai,” in ji shi.