Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce mika wuya da daruruwan mayakan Boko Haram suka yi, ya taimaka wajen farfadowar harkokin noma a wasu yankunan jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da Kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya da ke kula da sha’anin sojin kasar ya ziyarce shi a ranar Laraba a Maiduguri.
Kwamitin ya kai ziyarar ne karkashin jagorancin Sanata Mohammed Ali Ndume kamar yadda wata sanarwar da gwamnatin Bornon ta fitar ta ce.
A cewar Zulum, kashi 700 na manoman jihar sun samu damar komawa gonakinsu lamarin da ya kai ga farfdowar harkokin noma.
Gwamnan ya kara nuna goyon bayansa ga matakin amfani da karfin soji da kuma bin tafarkin siyasa wajen kawar da akidun mayakan da maido da su cikin jama’a.
Hare-haren Boko Haram da aka kwashe sama da shekaru goma ana fama da shi a jihar Borno, ya kassar fannin ayyukan noman jihar.
A watan Nuwambar 2020, wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun halaka manoman shinkafa akalla 40 a yankin Zabarmari da ke arewacin jihar Bornon