Kotun Ƙolin Amurka ta yi watsi da umarnin da Shugaba Joe Biden ya bayar da ya tilasta wa ma’aikata yin rigakafin annobar korona a manyan kamfanoni.
Kazalika umarnin ya tilasta saka takunkumi da kuma yi wa ma’aikatan gwaji a duk mako.
Alƙalan kotun sun ce umarnin ya shallake ƙarfin ikon da shugaban ƙasar ke da shi.
Sai dai sun yanke hukuncin cewa za a iya ba da wani umarnin maras tsauri na yin rigakafi ga ma’aikata a asibocin gwamnati.
Gwamnatin Biden ta dage kan cewa tilashin zai taimaka wajen yaƙi da cutar.
Shugaba Biden wanda farin jininsa ke raguwa a ƙasar, ya bayyana rashin jin daɗinsa da hukuncin da ya “daƙile tunani mafi sauƙi da zai kare rayuwar ɗan Adam ga ma’aikata”.
Ya ƙara da cewa: “Ina kira ga jagororin ‘yan kasuwa da su yi koyi da waɗanda suka ɗauki matakai – ciki har da ɗaya bisa uku na kamfanonin Fortune 100 – don su kare ma’aikatansu da kwastomi da jama’ar yankunansu.”