Sports
Barcelona ta ja kunnen Ousmane Dembele ko kuma ta sayar da shi
Daga kabiru basiru fulatan
Barcelona ta umarci Ousmane Dembele da ya saka hannu kan yarjejeniyar tsawaita zamansa a kungiyar ko kuma ta sayar da shi in ji Xavi.
Kwantiragin Dembele zai karkare a karshen kakar bana, inda Xavi ya ce wata biyar ana tattaunawa da dan kwallon, amma an kasa cimma matsaya ”Ba za mu yi ta jiransa ba.”
”Ko dai dan wasan ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da wasa a Camp Nou, ko kuma mu sayar da shi tun kan kwantitaginsa ya cika, ba mu da wani zabin.”
”Muna wani yanayi na kalubale, mun kuma fayyace komai ga Ousmane.”Dembele ya koma Barcelona daga Borussia Dortmund a 2017 kan fam miliyan 96.8, sai dai kuma dan wasan tawagar Faransa na faama da yawan jinya.
Ana ta alakanta shi da komawa Manchester United ko Newcastle ko kuma Liverpool masu buga babbar gasar tamaula ta Ingila.
”Yana son ya ci gaba da zama a Camp Nou, amma ba mu kulla yarjejeniya ba, yanzu a matakin da muke ko dai ya saka hannu ko kuma mu sayar da shi,” in ji Xavi, wanda ya karbi aikin jan ragamar Barcelona a cikin watan Nuwamba