News
Buni da Badaru sun jagoranci zaman sulhu tsakanin ɓangaren Ganduje da Shekarau a Abuja
Daga Yasir sani Abdullah
Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni tare da takwaransa na jihar Jigawa Abubakar Badaru da sauran masu ruwa da tsaki sun gana da jagororin jam’iyyar APC na Jihar Kano.
Buni ne ya kira taron, wanda aka gudanar a Abuja ranar Talata, domin sasanta bangarorin jam’iyyar biyu a Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.
Wasu majiyoyi sun shaidawa Daily Nigerian Hausa cewa, shugabannin jam’iyyar APC sun nuna damuwarsu kan rigingimun da suka dabaibaye jam’iyyar a Kano.
Ɗaya daga cikin mahalarta taron wanda ya zanta da Daily Nigerian Hausa bisa sharadin sakaya sunansa, ya ce jam’iyyar ta sha alwashin yin iya kokarinta na ganin ta kaucewa sake afkuwar irin abinda ya faru a jam’iyyar APC na Zamfara a Kano.
Dangane da shari’ar da ake yi a kotun ɗaukaka ƙara kuwa, shugabannin jam’iyyar sun nuna rashin jin daɗinsu kan yadda rikicin har ya kai ga kotu.
Ya ƙara da cewa shugabannin jam’iyyar sun kaucewa tattaunawa a kan shari’ar da ake tafkawa a kotu, inda su ka ce ko menene sakamakon shari’ar, kowane bangare na bukatar juna don samun nasara a zaɓe.
Daga nan aka ɗage taron zuwa ranar Talata mai zuwa domin ci gaba da tattaunawa.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan Yobe, Mamman Mohammed ya fitar, ya ce manufar taron ita ce a sulhunta shugabannin APC a Kano.
“A karshen taron, mahalarta taron sun taya juna murna tare da nuna gamsuwa da sakamakon taron.”
“Taron da aka yi a karkashin jagorancin Gwamna Buni na daga cikin matakan da jam’iyyar ta dauka na sasanta ‘ya’yan da ba su ji ba gani kafin babban taron kasa da ke tafe.
“Kwamitin Buni ya kuduri aniyar warware rigingimun da ke tafe don tunkarar taron tare da hadin kai.”
Jaridar Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa jam’iyyar APC a Kano na fama da rikicin cikin gida, inda bangarorin biyu ke gudanar da shiyya-shiyya, na kananan hukumomi da na jahohi.
Wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin Mai shari’a Hamza Muazu a karshen shekarar da ta gabata ta tabbatar da zaman majalisar unguwanni da na kananan hukumomi da bangaren Shekarau ya gudanar.
A bisa rashin gamsuwa da sakamakon, sai ɓangaren da Ganduje ya ɗaukaka ƙara, inda suka buƙaci a soke hukuncin da karamar kotun ta yanke.
Har yanzu dai ana ci gaba da shari’ar a kotun ɗaukaka ƙara.