News
Ledojin jini 500 ne su ka gurɓace sakamakon katsewar wutar lantarki a Abuja, inji NBSC

Daga yasir sani abdullahi
Hukumar Kula da Jini ta Kasa, NBSC, ta ce ledojin jini har guda 500 ne su ka lalace sakamakon katse wutar lantarki da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Abuja, AEDC ya yi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai da na hukumar, Haruna Abdullahi ya fitar.
“Ledar jin har 500 na jini da aka samu da ga masu ba da gudummawar jini ne su ka gurɓace sakamakon katsewar wutar lantarki a shalwatarmu.
“Katsewar wutar lantarkin kuma yana haifar da babban cikas ga masu ba da gudummawar jini na sa kai saboda haɗarin da ke tattare da tsaro da amincin su a matsayinsu na masu ba da gudummawar jini.
“A cikin kwanaki masu zuwa, matsalar karancin jini ga majinyata da ke bukatarsa za ta addabi ƴan Najeriya sakamakon katse wutar da hukumar AEDC ta yi, kuma idan ba a magance matsalar ba, to ba za a haifi ɗa mai ido ba” in ji hukumar.
Hukumar a cikin sanarwar ta baiyana muhimmancin samar da wutar lantarki gare ta, musamman ta fannin tabbatar da lafiyar jini kafin amfani da shi.
“Shawarar da AEDC ta yanke na katse wutar lantarkin hukumar a ranar 21 ga watan Janairu bayan mun biya wasu kudade a watan Disamba 2021 ya baiwa hukumar mamaki.
“Wannan ya fi ban mamaki ganin yadda kwanan nan hukumar ta biya kudaden da a ke bin ta,” in ji shi.