Connect with us

News

Zaɓen fidda gwani a Ekiti: Ƴan APC sun yi bore

Published

on

Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

Ƴan jam’iyyar APC a Jihar Ekiti sun gudanar da zanga-zangar adawa da yadda zaben fidda gwani na gwamna ya ke gudana a jihar.

A yau Alhamis ne a ka shirya gudanar da zaɓen.

Ƴan jam’iyar da su ka hallara a sakatariyar jam’iyyar su na zargin gwamnatin jihar, ƙarƙashin APC da rashin adalci a cikin wannan tsari.

Advertisement

Duk da cewa an fara tantancewa a wasu unguwanni, ƴan jam’iyyar da suka yi zanga-zanga a sakatariyar sun ce ba za su shiga cikin zaben ba.

ya’yan jam’iyyar sun yi ta ihu su na cewa “Ba zaɓe! Ba a zaɓen fidda gwani a Ekiti,” ‘

Wannan lamari dai na zuwa ne bayan Sanata kuma daya daga cikin masu neman takarar, Sanata Opeyemi Bamidele ya bukaci jam’iyyar APC da ta dakatar da yin zaɓen na fidda gwani a jihar.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *