News
Za mu faɗa wa gwamnati gaskiya idan ta kama – Sarkin Gaya
Daga kabiru basiru fulatan
A yau Asabar 29 ga watan Janairu ne gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje zai bai wa sabon sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim sandan girma.
An dai nada mai martaba Alhaji Aliyu Ibrahim ne a watan Satumban 2021 bayan rasuwar mahaifinsa sarkin Gaya marigayi Ibrahim Abdulkadir.
To shin ko mene ne sabon sarkin ya sanya a gaba domin ganin cigaban masarautar tasa?
Tambayar kenan da Khalipha Dokaji ya yi masa. To sai dai ya fara ne da bayan ikan yadda ya ji bayan an ayyana shi a matsayin sarkin na Gaya