News
Ciwon kunne ya sa an ɗage shari’ar ‘Ɗan Sarauniya’ Jin sa ya dauke
Daga Usman abdullahi jibrin
Wata kotu a Kano ta ɗage zaman farko da aka soma a yau bayan an gurfanar da tsohon Kwamishinan Ayyuka na jihar, Mu’azu Magaji.
Lauyan wanda ake zargin ya bayyana cewa an ɗage shari’ar ne sakamakon matsala da kunnen wanda ake zargin yake da shi biyo bayan hatsarin motar da ya yi a Abuja bayan yan sanda sun biyo shi.
Lauyansa, Barrista Garzali Datti Ahmad ya shaida wa BBC cewa sun gaya wa kotu cewa ba za a iya karanta wa wanda ake zargin laifinsa ba sakamakon ba ya ji sosai, ganin cewa a lokacin da ya yi hatsarin, balan-balan ta kariya wadda aka fi sani da “Airbag” ta fito ta daki kunnensa.
Ya bayyana cewa a halin yanzu kotu ta bayar da umarni a mayar da shi asibitin ƴan sanda da ke Bompai a Kano domin a ci gaba da duba lafiyarsa.
-
News7 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
Uncategorized2 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News5 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
