News
Dalibin Ajin Karshe A BUK Ya Rasu A Cikin Makaranta
Daga muhammad muhammad zahraddin
Wani dalibi dan ajin karshe a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ya yanke jiki ya fadi matacce da dakin kwanan dalibai da ke cikin jami’ar.
Hukumar Gudanarwar jami’ar BUK ta ce dalibin mai suna Babangida Ahmed ya yanke jiki ya fadi ne a yayin da yake shirin tafiya Sallar Asuba ranar Juma’a. Sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na Jami’ar Bayero ta Kano, Lamara Garba, ya fitar ta ce, “Dalibai sun shaida mana cewa Babangida ya fito daga dakinsa ne da misalin karfe 4.30 na asuba, inda ya yanke jiki ya fadi baya numfashi, tun kafin a garzaya da shi zuwa asibitin da ke cikin jami’ar; Ko da aka kai shi asibitin rai ya riga ya yi halinsa.”
Lamara ya ce, “Hukumar gudanarwar jami’ar ta sanar da mahaifan Babangida abin da ya faru, kuma za a kai gawarsa domin yi mata jana’iza bisa tanadin addinin Islama.”
Rasuwar Babangida, wanda ke karatu a Sashen Kimiyyar Adana Bayanai, ta zo ne kimanin wata biyu bayan rasuwar wani dalibi dan ajin karshe a jami’ar.
Jami’ar BUK ta bayyana cewa kafin rasuwar Babangida, ya kasance yana zuwa ganin likita a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, saboda wata rashin lafiya da ba a bayyana ba.
Marigayi Babangida Ahmed dan asalin Karamar Hukumar Misau ne daga Jihar Bauchi.