Connect with us

News

Mazauna Birnin Gwari sun ce ba sa iya bacci sai da rana saboda fargabar ‘yan fashin daji

Published

on

123052603 c0adc453 e1da 47e4 82d5 c055e70f24a5.jpg
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddini

Mazauna yankin Birnin Gwari da ke jhar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da kasancewa cikin fargaba, sakamakon ƙaruwar satar mutane, da hare-haren ƴan fashin daji a yankin.

Ko da a baya-bayan nan sai da aka yi garkuwa da mutane 17 a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari bayan barayin sun tare motocin da suke ciki.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC Hausa cewa duk da yake akwai jami’an tsaro a hanyar, masu garkuwa da mutane suna cin karensu babu babbaka a yankin.

Advertisement

Ya ce,” A ranar Juma’a masu garkuwar sun tare wasu motocin fasinja da ke kan hanyar zuwa Buruku, inda suka ɗauki mutum bakwai wadanda ‘yan kasuwa ne da suka je cin kasuwa.

”A washe garin da aka sace mutanen ma wasu ‘yan fashin dajin sun sake tare hanya inda suka dauki mutum goma, daga bisani daya daga cikinsu ya gudo inji mazaunin yankin.

Mutumin ya ce dama jama’ar yankin nasu ba sa bacci yana mai cewa “idan dai mutum na son ya yi bacci to sai dai ya yi da rana, saboda kullum a cikin zulumin abin da zai iya faruwa muke.”

Advertisement

“Ba a yin kwana uku a jere ba a sace mutane a hanyar Birnin Gwari ba, wannan abu yana damunmu matuka, muna so gwamnati ta kara jami’an tsaro a wannan hanyar,” in ji mazaunin yankin.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *