News
Galibin ‘Yan Siyasar Nijeriya ‘Yan Kwaya Ne da Masu Damfara a Intanet – Gwamnan Anambra
Daga Yasir sani abdullahi
Soludo, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, wanda ya lashe zaben gwamnan Anambra a ranar 6 ga watan Nuwamba, 2021 a karkashin jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), yayi wannan maganar ne a ranar Asabar.
Ya ce siyasa ta zama babbar kasuwa a Najeriya, inda ya ce da dama daga cikin su akwai barayi, masu shan kwayoyi da masu damfarar Intanet kuma dukkansu sun shiga siyasa don gudun kada a kama su.
“Siyasa ta zama babbar kasuwa, Zaɓabbe da nadadde da manyan ma’aikatun gwamnati sun dauki siyasa wajen ‘cin abinci’ da wawason kudade maimakon a mayarda hankali ga hidumtawa jama’a”. Inji shi