Wasu zakuna biyu da ake kulawa da su a wani gidan zoo sun kashe mutumin da yake ba su abinci.
Shaidu a gidan kulawa da namun dawa a birnin Arak na kasar Iran sun ce zakunan sun tsere daga kejin nasu bayan sun kashe mutumin.
Jami’ai sun ce ‘yan sanda da ma’aikatan kula da muhalli sun yi nasarar kama namun dajin daga baya kuma sun mayar da su kejin nasu ba tare da sun raunata su ba.
Gidan kula da namun dawa na Arak na cikin mafi girma a kasar Iran.