News
Gwamnatin Taraiya ta yi ƙarin kuɗin tafiye-tafiye na ma’aikatan gwamnati
Daga kabiru basiru fulatan
Gwamnatin Taraiya ta amince da ƙarin kuɗin tafiye-tafiye da a ke baiwa maikata, wanda a turance a ke kira da ‘Duty Tour Allocation’, DTA
Shugaban Hukumar kula da Albashi da Haƙƙoƙin Ma’aikata ta Ƙasa, Ekpo Nta ne ya baiyana hakan ga manema labarai a Abuja a jiya Alhamis.
Nta ya ce sabon ƙarin ladan tafiye-tafiyen zai fara aiki ne da ga 1 ga watan Fabrairu, inda ya baiyana farin ciki game da ci gaban da a ka samu.
“Wannan wani tagomashi ne ga ma’aikata. Gwamnatin Taraiya na ƙoƙarin kyautata walwalar ma’aikata.
“Ma’aikata da ke matakin albashi na 01 zuwa 01 yanzu za su riƙa karɓar N10,000, daga mataki na 05 zuwa 06 kuma N15,000, su kuma na mataki 07 zuwa 10 za su riƙa karɓar N17,500.
“Haka kuma masu matakin albashi na 12 zuwa 13 za su riƙa karɓar N20,000, na matakin 14 zuwa 15 kuma za su samu N25,000, inda mataki na 16 zuwa 17 za su riƙa karɓar N37,000,” in ji shi.
Nta ya tuna cewa, a baya, DTA ɗin ma’aikaci mai matakin albashi na 06 zuwa ƙasa N5,000 ne, yayin da na mataki 07 zuwa 14 N12,000 ne, sannan na matakin albashi 15 zuwa 17 N16,000 ne.
Ya yabawa Gwamnatin Taraiya da a kullum ta ke kula da walwalar ma’aikatan ta.
Shugaban ya kuma yabawa kafafen yaɗa labarai a bisa ƙoƙarin su na ilmantar da al’umma, inda ya hore su da su ɗore da kyawawan aiyukan da su ke yi