News
Maza na ɗaukar hutu a wajen aiki domin rainon jarirai a Australia
Daga kabiru basiru fulatan
Wani sakamakon bincike da gwamnati ta saki ya nuna cewa iyaye na biya domin a basu hutu a ma’aikatu domin su kula da jarirai a Australia.
Wannan na nuni da yadda a ke sauka da ga al’adar rainon jarirai da iyaye ke yi a ƙasar.
A wata ƙididdiga ta ƙidayar al’umma ta 2020 da 2021 da Hukumar Daidaita tsakanin Jinsi a Wajen Aiki (WGEA) ta fitar, ya nuna cewa a duk ma’aikatu biyar, masu ɗauke da ma’aikata a ƙalla 100, uku na biya domin a basu hutu domin rainon jarirai a Australia, kuma ga kowanne jinsi.
Daraktan WGEA, Mary Wooldridge ta baiyana cewa wannan matakin zai ƙara haɓɓaka harkar kula da ƴaƴa, in da hakan ke da amfani ga al’umma.
Hakazalika, canje-canje da a ke samu a dokokin aiki ne ke sa yawa a na samun ƙaruwar iyaye maza na ɗaukar nauyin rainon ƴaƴa.
Duk da cewa har yanzu iyaye mata su su ka fi yawa a rainon ƴaƴa, adadin iyaye maza da ke rainon ƴaƴa na samun ƙaruwa har ya kusa ruɓanya na 2020 zuwa 2021 da ga kashi 6.5 zuwa kashi 12 cikin ɗari.