News
Tsohon ɗan majalisar wakilai ya zama hadimin matar shugaban ƙasar Nijeriya

Daga yasir sani abdullahi
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa Sani Zorro a matsayin Babban Mai Taimaka masa na Musamman a kan Dabarun Hulɗa da Jama’a a ofishin Matar Shugaban Ƙasa.
Jaridar indaranka ta rawiato cewa shi dai Zorro tsohon ɗan majalisar wakilai kuma ɗan jarida ne.
Babban Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Harkar Yaɗa Labarai, Garba Shehu je ya tabbatar da naɗin a wata sanarwar da ya fitar a yau Asabar a Abuja.
Shehu ya ce Zorro zai yi amfani da ɗumbin ƙwarewarsa a aikin jarida ta shekara da shekaru, inda ya yi wallafe-wallafe da dama sannan ya riƙa muƙaman ƙungiya a matakai daban-daban.
Ya ƙara da cewa Zorro ya yi Shugabancin Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Ƙasa, NUJ, Ƙungiyar Ƴan Jarida ta Afirka-maso-Yamma da kuma Taraiyar Ƴan Jaridar Afirka.
In ji Shehu, Zorro ya rike shugabancin kwamitin kula da harkokin ƴan gudun hijira a Arewa-maso-Gabas lokacin ya na ɗan majalisar wakilai.
Garba Shehu ya kuma sanar da da sauyin wajen aiki na masu muƙaman siyasa uku da ga ofishin Matar Shugaban Ƙasa zuwa ofishin Sakataren Gwamnatin Taraiya kafin da ga bisani a kai su wasu hukumomin da ma’aikatun su ci gaba da aiki a can.