News
NAZIRU SARKIN WAKA ZAI BA WA LADIN CIMA MILIYAN 2.

Daga kabiru basiru fulatan
Naziru sarkin Waka yayi alkawarin bai wa dattijuwar masana’antar KANNYWOOD Ladin Cima kyautad Naira Miliyan 2 domin ta ja jari.
Haka zalika ya kuma dau alkawarin bai wa Fati Slow Motion Naira Miliyan Daya.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ta ci gaba da musayar zafafan kalamai tsakanin mawakin da jagoririn masana’antar KANNYWOOD biyo bayan fallasar da Ladin Cima tayi.