Daga muhmmad muhmmad zahraddin
Hukumar Hisbah a Kano ta kama mutum 78 maza da mata bisa zargin za su yi auren jinsi.
An kama su ne a Unguwar Nasarawa GRA a wani gida da ake kira White House.
Yanzu haka mutanen da aka kama suna hannun hukumar Hisbah. A cikin gidan an samu tarin kwaroron roba.
Sai dai matasan sun musanta zargin da ake yi musu na za su yi auren jinsi ko kuma suna halartar bikin, inda suka ce taron murnar ranar zagayowar haihuwar ɗaya daga cikinsu suke yi.