News
Mu ba ma cikin yajin aikin ASUU — Jami’ar Abubakar Audu
Daga kabiru basiru fulatan
Malaman Jami’ar Prince Audu, PAAU, a yau Laraba sun baiyana cewa ba za su shiga yajin gargadi da Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa, ASUU ta shiga yi na tsawon wata ɗaya ba.
Farfesa Ogunbiyi Joseph, Shugaban Tsangayar Ilimi ta jami’ar ne ya baiyana hakan a yayin tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai, NAN.
Ya ce jami’ar ba taa shiga yakin aikin da ASUU ta fara a ranar Talata ba.
Ya ce tafiya yakin aikin ya zama rashin halarci ga Jagoran Jami’ar, Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.
A cewar Joseph, gwamna Bello ya na baiwa malaman jami’ar ta PAAU duk abinda ASUU ta nema da ga Gwamnatin Taraiya sabo da kar su tafi yakin aiki.
Ya ƙara da cewa malaman jami’ar su na jin daɗi sabo da a na kula da walwalarsu, inda yara ƙara da cewa shi ya sa ma ba a samun cikas a manhajar karatu ta jami’ar.
Joseph ya baiyana cewa a yayin bikin yaye ɗalibai karo na 6, Gwamna Bello ya sanar da baiwa jami’ar cin gashin kan ta, inda hakan na nufin ita za ta riƙa samar da kuɗin shiga a wani mataki na gata da gwamnan ya yi mata.