News
Masu bincike sun gano sabbin jinsi 10 na jemage a wani daji a Nijeriya

Daga yasir sani abdullahi
Wasu masu bincike sun baiyana cewa sun gano jinsi goma na jemage a wasu dajika a Nijeriya waɗanda ba a taɓa ganin irin su ba a baya
Masu binciken sun baiyana haka ne a wata sanarwa da Manajar yaɗa Labarai ta Hukumar Kula da Ƙananan Dabbobi , SMACON, Esther Nosazeogie ta fitar.
Jagoran masu binciken, Irori Tanshi , wanda ya lashe lambar girma kan ilimin jemagu, shi ke ya gano jinsin bayan ya shafe watanni 15 ta na nazari bayan ta yi amfani da wasu tarkuna na kama jemage.
Hukumar ta ce Tanshi da abokan aikin ta sun kutsa cikin Gandun Namun jeji na ‘Afi Mountain Wildlife Sanctuary’ da kuma ‘ Cross River National Park’ (Okwangwo Division) a jihar Cross River da ga watan Mayu 2015 zuwa Janairun 2018 domin yin nazari mai zurfi a kan jemagu.
Rahoton ya ce shekarun baya, jinsin jemage 90 a ka sani a Nijeriya.