News
Aljeriya Za Ta Biya Matasa Marasa Aikin Yi Naira 41,500 alawus-alawus a duk wata
Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban kasar Aljeriya, Abdelmadjid Tebboune ya bayyana shirin gwamnatinsa na bullo da biyan alawus-alawus ga matasa marasa aikin yi a kowane wata.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar arewacin Afirka ke fama da rashin aikin yi da kusan kashi 15 cikin dari.
Najeriya mai yawan marasa aikin yi sama da kashi 50% na al’ummarta, a kalla Najeriya na da mutane kusan miliyan 200.
Da yake magana a gidan talabijin na Aljeriya kamar yadda aka nakalto a labaran Larabawa, Tebboune ya ce wadanda suka ci gajiyar tallafin, masu neman aiki ne masu shekaru 19 da 40 ya kara da cewa za a fara biyan kudin ne a watan Maris.
Ya ce wadanda suka cancanta za su iya karbar kusan dala 100 (N41,576) duk wata, da kuma wasu kudaden jinya , har sai sun sami aiki.