Connect with us

News

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kama mutane 6 da laifin sayar da litar mai sama da N165 a Kano

Published

on

FB IMG 1644997529677
Spread the love

Error: Contact form not found.

Daga yasir basiru fulatan

 

 

Advertisement

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta kama wasu manajoji hudu da wasu ma’aikatan mai guda biyu da laifin sayar da man fetur sama da farashin lita na N165 a jihar.

Da yake magana a wani taron manema labarai, wanda a ka gudanar a ofishinsa a jiya Talata, shugaban riƙon ƙwarya na hukumar, Mahmoud Balarabe, ya ce an kama mutanen ne a gidajen mai daban-daban da ke cikin birnin Kano.

A cewar sa, hukumar ta samu ƙorafe-korafe da dama da ga mazauna jihar cewa duk da ƙarancin man fetur da a ke fama da shi, wasu gidajen mai na sayar da shi lita ɗaya tsakanin N200 zuwa N208 a jihar.

Advertisement

Balarabe ya ce da karɓar koken, hukumar ba ta yi wata-wata ta fara sunturi, inda ta je wasu gidajen mai da ke cikin kwaryar birnin Kano, ta kuma gano wasu da ga cikinsu su na sayar da man fetur a kan Naira 200 da kuma N208 a ko wacce lita.

“A yayin sumamen, mun kama manajoji 4 na gidajen mai. An kama mutum daya a lokacin da yake taimakawa manajan gidan mai wajen canja litar sama da N165.

“Dayan ma’aikacin mai ne kuma mun kama shi bayan manajan nasa ya haura katanga ya gudu.

Advertisement

“Akwai wani gidan mai da muka gano cewa sun riga sun sayar da lita 18,000 akan Naira 200, inda suka samu Naira 630,000 a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. An gano dayan gidan mai yana ɓoye sama da lita 4,000. Mun tilasta musu su ci gaba da sayar wa jama’a lita 4,000 da su ka ɓoye,” inji shi.

Balarabe, a bayyane ya nuna fushinsa kan lamarin, ya ce hukumar za ta binciki wadanda ake zargin tare da mika su ga hukumomin da suka dace domin daukar mataki.

Ya koka da cewa, duk da sake farfado da layukan mai a jihar, manajojin gidajen man na ci gaba da gallazawa mutane ta hanyar canja litar man fetur sama da farashin da aka kayyade na N165.

Advertisement

Ya kuma i alwashin cewa hukumar ba za ta lamunci abin da suffanta shi da “ayyukan cin hanci da rashawa” ba, inda ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da gudanar da sumamen har sai ta kawar da duk wani abu da bai dace ba a tsakanin jama’a.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *