Sports
PSG ta doke Madrid 1-0 a mintin karshe a Paris

Daga muhmmad muhmmad zahraddin
PSG ta doke Madrid 1-0 mai ban haushi a zagayen kungiyoyi 16 a birnin Paris.
Dan wasan gabanta Kylian Mbappe ne ya saka kwallon daya tilo yan dakikai a bushe wasan.
Mbappe wanda Madrid ta sha alwashin daukowa a karshen kaka ya nuna kansa a wasan, bayan da ya yanka masu tsaron baya biyu ya kuma saka wa gola osi a minti na 90+4.
Kadan ya rage a tashi 2-0, don kuwa Lionel Messi ya barar da Fenareti a minti na 62.
Hakan na nufin Madrid na bukatar kwallo biyu a zagaye na biyu a wata mai zuwa kafin taga bayan PSG a Bernabeau.
A daya wasan Manchester City ce ta ragargaji Sporting Lisbon har gida da ci biyar.
Bakin basu bata lokaci ba don tun a minti na bakwai da sa wasa suka fara aiki ta hannun Riyad Mahrez, sai kuma Bernando Silva yasa kwallo biyu, Phil Foden ya kara daya tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Jim kadan bayan dawowa ne Raheem Sterling ya saka tasa, kuma da haka City ta hada kwallayen biyar inda za ta jira Sporting ta same ta Etihad wata mai zuwa.
A gobe kuma za a ba hamata iska ne tsakanin Liverpool da Inter Milan a filin San siro a Italiya.
A dayan wasan Red Bull Salzburg ce za ta karbi bakunci Bayern Munich a Jamus.