Sports
Man United ta ci Brighton 2-0, ta dawo na hudu a Premier

Daga muhmmad muhmmad zahraddin
Cristiano Ronaldo ne ya ci kwallon farko bayan an dawo hutun rabin lokaci, a wasan farko da United taci cikin wasanni hudu.
Jim kadan bayan haka mai tsaron bayan Brighton Lewis Dunk ya karbi jan kati.
Kuma kamar za su rama a minti karshe United ta kai kora ta hannun Bruno Fernandez, wanda ya gar gola kafin saka kwallon ta biyu a mintin karshe.
Sai a wannan karon Ronaldo ya ci kwallo a wasanni shida da ya buga wa United.